452
Saboda Martaba da girma na watan Azumin Ramadan tare da kuma tausayawa da kulawa ga ma’aikata jihar Sakkwato , kananan hukumomi da sauransu, ya bayar da damar a biya wani sashe daga cikin Albashin kowane ma’aikachi daga jiya lahadi domin saukakawa ga al’amurran yau da kullum a cikin Azumi. A Jawabin Gwamnan da Yayi kan batun biyan kudin ga ma’aikata jihar ya ce "muna matukar son ganin farin ciki a fuskokin al’ummar jahar sokoto" Wannan abin alherin da gwamnan ya Yi ya ma’aikatan jihar da ma ‘yan kasuwa suna ta yabawa da fatan alheri.


