*Shugaba Tinubu Ya Kaddamar da Shirin gina dubban gidaje ga yan Najeriya*
A wani gagarumin biki da aka gudanar a babban birnin tarayya, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci sanya harsashin ginin sabon Birnin Renewed Hope wanda zai kunshi gidaje masu saukin farashi don saukaka mallakar muhalli ga ‘yan kasa
Shi dai shirin na samar da dubban gidajen zai karade ilahirin kasar ne a kokarin gwamnati na ganin an saukaka wa ‘yan kasa hanyoyin mallakar gidaje da ababen more rayuwa a fadin Najeriya.
Shirin wanda Ma’aikatar Gidaje da Raya Birane ke jagoranta, ya kudiri aniyar fara shirin da gina gidaje 50,000 a matsayin somin-tabi ta hanyar samar da kudade da ga wani kaso a kasafin kudi da hadin gwiwa tsakanin gwamnati da hukumomi masu zaman kansu.
A yayinda yake jawabi wajen kaddamar da shirin Shugaba Tinubu ya jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da gidaje masu inganci ga daukacin ‘yan Najeriya a matsayin daya daga hanyoyin bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi. Shugaban ya kara dacewa samar


