Shekara bakwai kamfanonin shinkafar Abuja su na wahala da mutane kawai a barsu su goga da ’yan kasuwa a samo abinci daga waje farashi ya sauka mayaudara su ji kunya. Baza su iya ciyar da Nijeriya ba a farashi Mai sauki.
Duk sune ke raba kuɗi suke saye abinci tun yana gona alhali sun karɓi manyan filaye da sunan za su yi noma sun kasa sun bar mutane a cikin azaba.
Ka ɗauki misalin idan Saudiyya suka ce ba za su sayo abinci daga waje ba me zai faru. Dole su wahala to haka muma da gangan suka yi.
Idan Allah ya baka kuɗi ya baka rayuwa har aljanna za ka nema da su balle abincin da za a ci. Mun daɗe muna faɗa idan ba an buɗe kasa kayan buƙata sun shigo ba haka za a yi ta wahala.
Ma’aikatan iyakokin ƙasa na arzuta kansu da cin hanci ana shigo da kayan ta simogar wasu shafaffu da mai ana tsiyata kananan ’yan kasuwa marasa gata.
A bar kamfanonin shinkafar su mutu kawai mutane su rayu don kada yunwa ta sa a bijirewa hukuma, dama ba Nomar suke yi ba abinci da talaka ya noma suke saya su gyara su sayar tsada.
An ba su manyan filaye sun maida su kadarar su, sun karɓe kuɗin CBN sun kwanta a kai su da iyalansu sun bar talakawa na wahala kullum cewa suke za su sauke farashin kayan abinci alhali karya suke yi.
Daga Muazu Harɗawa, Editan Jaridar Alheria Bauchi. 08062333065.

