A ranar Talatar da ta gabata Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da shirin bada tallafi ga ‘yan ƙasa na ‘Renewed Hope Conditional Cash Transfer’, shirin da ake sa ran magidanta miliyan 15 za su amfana da shi.
An ƙaddamar da shirin ne a Fadar Villa da ke Abuja albarkacin Ranar Yaƙi da Talauci ta Duniya ta bana.
Yayin ƙaddamar da shirin, Shugaba Tinubu ya miƙa cekin N25,000 ga wasu daga cikin waɗanda za su ci gajiyar shirin: Larai Suleiman, Shuaibu Hassana, Sariki Bala Gamu, Okor Jonah da kuma Hameed Kosemani Isiaka.
Wakilin Tinubu a wajen taron kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya ce gwamnatin tarayya na da tsare-tsaren da ta shirya domin wadata ƙasa da abinci, kawo ƙarshen yunwa, samar da ayyuka, daƙile talauci da inganta tsaro da sauransu.
A cewar Tinubu, “Gwamnatina za ta jagoranci tabbatar da ‘yan Nijeriya sun samu damammakin ayyuka masu gwaɓi da kuma kyautatuwar rayuwa.
“A yau, gwamnatina ta ƙaddamar da Shirin Renewed Hope Conditional Cash Transfer don tallafa wa marasa galihu wajen rage raɗaɗin tallafin mai da aka cire da sauran ƙalubalen tattalin arziki,” in ji shi.
Da take jawabi a wajen taron, Ministar Jinƙai da Yaƙi da Talauci, Dr Betta Edu, ta ce juya wa batun yaƙi da talauci baya tamkar jefa ƙasa cikin wani mummunan yanayi ne.
Ta ce, N75,000 da Shugaba Tinubu ya sanar za a raba wa magidanta a faɗin ƙasa, ya isa assasa ƙaramar sana’a don kyautata rayuwa.
Ta ƙara da cewa, “Bayan wannan, gwamnati za ta samar da muhalli masu sauƙin kuɗi don amfanin talakawa da kuma waɗanda rikici ya ɗaiɗaita don samun matsuguni.”
Sauran tsare-tsaren bada tallafin da gwamnati ta shirya in ji Ministar, sun haɗa da koyar da ƙananan sana’o’i da sauransu, duka dai da zummar yaƙi da talauci ta kowane ɓangare.

