An sako jagoran neman kafa ƙasar Yarabawa, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho, bayan shafe shekara biyu yana tsare a gidan yarin ƙasar Benin.
Igboho ya tabbatar da sakin nasa ne a shafinsa na Instagram inda ya wallafa cewa, “Sako ni daga Jamhuriyar Benin.”
Majiyarmu ta ce Igboho ya yaba wa waɗanda suka taka rawa wajen sako shi da aka yi, da suka haɗa da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo da fitaccen marubucin nan, Wole Soyinka da Farfesa Banji Akintoye da Ayo Adebanjo da sauran sarakunan gargajiya.
Idan dai ba a manta ba, a ranar 19 ga Yulin 2021 ‘yan sandan ƙasa da ƙasa suka tsare Igboho a Babban Filin Jirgin Saman Cadjèhoun da ke Cotonou, Jamhuriyar Benin, a lokacin da yake ƙoƙarin tsallakewa zuwa Jamus.
Ya tsere daga Nijeriya ne bayan samamen da jami’an DSS suka kai gidansa da ke Soka, Ibadan, Jihar Oyo, inda ake zarginsa da ɓoye tarin bindigogi.

