Home Labarai Buhari Ya Shiga Rayuwar Nadama Kan Yadda Yayi Mulkinsa — Solomon Dalung

Buhari Ya Shiga Rayuwar Nadama Kan Yadda Yayi Mulkinsa — Solomon Dalung

by Muhsin Tasiu Yau

Buhari mutumin kirki ne wanda ya aminta da makusantansa amma suka bata masa suna.

Alfijir Labarai ta rawaito tsohon Ministan Wasanni da Ci gaban Matasa, Solomon Dalung, ya yi ikirarin cewa a halin yanzu tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana rayuwar nadama kan yadda makusantansa suka bata masa suna a lokacin shugabancinsa.

 

Dalung wanda ya yi aiki a gwamnatin Buhari, ya ce gwamnatin ta gaza wajen cika alkawuran da ta daukarwa ‘yan Najeriya a lokacin yakin neman zabe na shekarar 2015.

A hirarsa da gidan Radio Trust, tsohon ministan ya ce a matsayinsa na wanda suka kafa jam’iyar APC ya zama wajibi ya fadi gaskiyar abin da ke faruwa.

Babuwani lungu da sako na kasar nan ba mu shiga a lokacin yakin neman zabe ba musamman a Arewacin Najeriya, mun dauki alkawura amma babu alkawarin da muka iya cikawa.

“Idan aka waiwaya baya, za a lura cewa babu wani abu da muka tsinana a lokacin gwamnatinmu.”

Ya ce a lokacin yakin neman zabe, sun yi wa ‘yan Najeriya alkawarin samar da tsaro da farfado da tattalin arzikin kasar da kuma yakar cin hanci da rashawa, amma sai dai sun gaza cika duk alkawuran da suka dauka.

Related Posts

Leave a Comment