Home Labarai Matsalar Tsaro: Mutane Dubu 23 Sun Bace a Nijeriya

Matsalar Tsaro: Mutane Dubu 23 Sun Bace a Nijeriya

by masta

Daga: Nafiu Salisu

Ƙungiyar agaji ta (Red Cross) a Nijeriya, ta fitar da sabuwarƙididdiga a kan yawan mutanen da suka mutu ko ɓata a Arewacin Nijeriya sakamakon ayyukan ‘yan ƙungiyar Boko haram a Borno da sauran jihohin Adamawa da Yobe.

Ayyukan ƙungiyar ‘yan tada ƙayar bayar ta Boko Haram da na ɓarayin daji masu riƙe da makamai ya haifar da rasa dubban rayukan mutane da asarar dukiya, muhalli da dama a gabaci da Arewacin Nijeriya, abin da ya haifar da koma-baya a faɗin ƙasar sakamakon ɗaiɗaita harkokin noma da kiwo musamman ga mazauna karkara.

Iyalai da dama ne ke kokawa tare da bayyana halin ƙuncin da suke ciki a dalilin rasa ‘yan uwansu da suka yi shekaru da dama a sakamakon ayyukan ‘yan ta’adda a Nijeriya.

Rahoton ƙungiyar taimakon ta Red Cross, ta ce ta haɗa wasu mutanen da suka ɓata da ‘yan uwansu bayan sun yi nasarar haɗuwa da su a yayin gudanar da ayyukanta na bada agaji wasu yankunan da ayyukan ‘yan ta’addar ya shafa, ta kuma ƙara da cewa, tana ci gaba da ƙara ƙaimi wajen gano waɗanda suka ɓace domin haɗa su da ‘yan uwan nasu.

Duk da cewa Gwamnatin Nijeriya da jami’an tsaron ƙasar suna bayyana galabar da suke samu wajen yaƙi da ‘yan ta’adda, to sai dai har yanzu ayyukan ta’addacin na ƙara ci gaba da faruwa a Nijeriya, inda a ke ƙara samun ‘yan gudun hijira da suke ƙara kwararowa cikin birane, musamman daga jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto, Kaduna da jihar Niger.

Nafiu Salisu

Related Posts

Leave a Comment