Tattalin Arziki: Manoma a Jihar Agadez Jamhuriyar Nijar Sun Shiga Tsaka Mai Wuya
Daga: Nafiu Salisu
Manoman albasa a jihar Agadez da ke jamhuriyyar Nijar, sun bayyana damuwarsu dangane da iyakokin ƙasa-da-ƙasa da ke rufe har yanzu, tun bayan juyin mulkin da sojojin ƙasar suka yi.
Iyakokin ƙasar da suke rufe dai sun haɗar da; Benin, Burkina Faso, Mali da Cote Dvoive. Waɗannan manoman albasa dake garin Agadez, suna kai albasar da suka noma zuwa waɗannan ƙasashe da ke makwaftaka da jamhuriyar ta Nijar.
A ranar 26 ne ga watan Yulin da ya gabata ne a wannan shekara ta 2023 sojojin ƙasar Nijar suka kifar da Gwamnatin Mohammed Bazoum, ƙarƙashin jagorancin shugaban tsaron fadar shugaban ƙasar, Col. Abdurrahman Jani.
Haka zalika manoman sun bayyana irin asarar da suka tafka a sakamakon rufe iyakokin ƙasar Nijar ɗin da sauran ƙasashe makwafta, sun kuma ce kafin juyin mulkin da aka yi a ƙasar Nijar ɗin, kullum suna fitar da manyan motocin albasa biyar zuwa ƙasashe Burkina, Mali da Benin. Sun kuma bayyana makudan kuɗin da suke samu idan sun shigar da albasar, da kuma kuɗin haraji da ƙasar Nijar ɗin ke samu.
Daga ƙarshe manoman albasar sun yi kira ga Gwamnatin Col. Abdurrahman Jani da sauran ƙasashen Burkina da Mali su duba halin da suke ciki a buɗe iyakokin ƙasar domin su sami damar shigar da albasar tasu don kar suyi asara.
Nafi’u Salisu


