Home Labarai Yadda Tsafta ke Neman Gagarar Garin Kano a Yau! Laifin wa ye?

Yadda Tsafta ke Neman Gagarar Garin Kano a Yau! Laifin wa ye?

by masta

Birnin kano a shekarun baya yana daya daga cikin birane goma da suka kowanne birni tsafta a nahiyar Afrika, a yanzu birnin ya koma cikin birane goma mafiya datti a nahiyar Afrikan injin binkicen hukumar kula da muhalli yana nan a cikin kundin bayanansu sunsa.

Akwai hukumomi da gwamnati ta samar da suke da alhakin kulawa da kwashe shara da tsaftar muhalli tare da kafa dokoki misali anan jahar kano muna da hukumar REMASAB alhakinta ta kula da tsaftace muhalli sannan akwai hukumar PPP “Polluter Pay Principle”‘ hukuma ce da take sa doka tare da cin tara ga duk wanda ya zubar da shara a wajen da bata kamata ba.

Birnin kano ya bunkusa da yawan al’umma wanda ya kamata ace gwamnati ta bullo da sababbin dabaru na zamani na kula da muhalli misali wayar da kan al’umma dole ne sai al’umma sun shigo tare da bada gudummursu akai wajen samar da kwamitin unguwa da zasu dinga lura da inda za’a zuba shara ba ko ina ba ita kuma tazo ta kwashe sannan ta sarrafa sharar ta dada samarwa da jahar kano kudin shiga kamar yacce wasu kasashen sukeyi.

A kokarin da gwamnati takeyi wanda ya kamata a yaba mata shine wajen kokarin dawo da motocin kwashe da tsohuwar gwamnati mai tafiya ta tafi dasu tare da samar da wasu sababbi, sannan akwai hukumar Kano Acresal da take kokarin ganin ta kawar waeda al’umma irin wadannan “Velnurable Disaster that’s harmful effects the Environment and community in general”.

~Jamil Iliyasu Bichi.

Related Posts

Leave a Comment