Home Labarai Shugaban Kasar Nijeriya Tinubu ya Sauke Nauyi Kallo ya kuma Koma ga Wadanda aka dorawa Nauyi a Arewa

Shugaban Kasar Nijeriya Tinubu ya Sauke Nauyi Kallo ya kuma Koma ga Wadanda aka dorawa Nauyi a Arewa

by masta

APC A YAU

Daga
Bilkisu Yusuf Ali

Tun a lokacin yakin Neman zabe shugaba Tinubu ya sha nuna kauna da Jan al’ummar arewa a jiki a duk inda ya sa kafa. Ko bayan an kammala zabe Allah ya ba shi nasara maganar Tinubu a kullum shi ne yadda za a dawo da martabar arewa da yadda arewa za ta samu cigaba musamman a abin da ya shafi tsaro da Noma da tattalin arziki. Za a yarda da wannan kuwa in aka kalli kunshin ministocinsa da SSA dinsa da SA da Shugaban Jam’iyya da ma muhimman mutanen da ya ja a gwamnatin duk dai don Jin Dadin arewan. Yanzu dai idanu Sun koma kan masu ruwa da tsaki a wannan gwamnati. Masu iya magana da ma Sun ce dillalin Wada shi ya San kudin jariri. Matsalolin arewa ga Su nan an San su don haka aka ba wa Wadanda suka fito daga gindin maganin don su kawo karshen damuwar.

Related Posts

Leave a Comment