APC A YAU

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, a ranar Litinin 21st Agusta, 2023 ya kaddamar da kwamitoci uku da za su kara inganta ayyukan jihar domin ta kara inganta.
Cikin kwamitocin akwai na yadda za a aiwatar da tsarin asusun bai-daya daya na jiha TSA. Kwamitin mai mambobi 12, na da Muhammad Aminu Isyaku a matsayin shugaba sai Salisu El Ladan a matsayin Sakatare.
Daga cikin nauyin da aka dora wa kwamitin akwai yin bita ga tsarin asusun gwamnati da kuma tsara yadda sabon asusun na bai-daya zai yi aiki da sauransu.
Kazalika, akwai kwamitin inganta tsarin biyan fansho da gratuiti ga ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi da suka ajiye aiki.
Kwamitin na da mambobi 12, da Dr Faruq Aminu a matsayin shugaba, sai Mukhtar Ammani a matsayin Sakataren kwamitin.
Daga cikin nauyin da aka dora wa kwamitin, akwai binciko hakikanin yawan ‘yan fanshon da ake da su a halin yanzu tsakanin jiha da kananan hukumomi da ba gwamnati shawara kan yadda za a kara inganta fansho a jihar Katsina da sauransu.
Sai kuma kwamitin da aka kaddamar don binciko gandun daji mallakin gwamnati, shi ma mai mambobi 12. Alhaji Khalil Bako ne zai jagoranci kwamitin da ofishin Gwamna a matsayin Sakatariya.
Daga cikin nauyin da aka dora wa kwamitin akwai gano gandayen dajin gwamnati da aka bayar domin gudanar da noma da yin bitar wadanda aka ba gonakin da sauransu.
Kwamitocin uku na da tsawon makonni hudu su gabatar da rahotaninsu.
SSA Isah Miqdad
21/08/2023

