Tarihinmu abin alfaharinmu
Tare da
Bilkisu Yusuf Ali
TARIHIN MALAM ALIMI DA KAFUWAR MASARAUTAR ILORIN
Malam Almi asalinsa Bafulatani ne yana daga cikinFulani Tokarawa. An hafe shi a shekarar 1740 a garinTonkara da take kasar Nijar. Ainhin sunansa Al-Salih, daga baya saboda sanin ilimin addininin Musuluncikuma kasancewarsa malami sai almajiransa suka canzasuke kiransa da Sheikh Alimi da Malam Alimi. Anhaifi mahaifin malam Alimi a garin Bunza kusa da brnin Kebbi. Sunan mahaifinsa Muhammadu Zubairu. Shehu Alimi ya yi karatunsa na addinin Musulunci a wajen malaminsa ake kiransa Jibril Bin Umar wandashehu Usmanu ya y karatu a wurinsa. Malam Alimi yanemi ilimi da yada addinin Musulunci ya ziyarcigaruruwan Gobir da Agadaz daga nan ya wuce harzuwa kasashen Yarbawa shi da jama’arsa dominjihadin yada addinin Musulunci gari-gari,. Daga nan yabiyo ta garin Ikoyi zuwa Epe zuwa Oyo zuwa Saki harzuwa garin Igbohoho daga nan ya ‘Yan’uwansa Fulani da ya tarar wadanda su suka a shi masauki shi da jama’arsa. Malam Alimi ya ci gaba da ilmantar da jama’a wadanda suka zo neman ilimi wajensa. A hankula wannan malami sai bakidayan wadannanal’ummomi da ya tarar a Ilorin suka ba shi giyon baya, musamman Hausawa da Fulani da Kanuri da Gobirawadomin cigaba da jihadin zuwa sauran qasashenYarbawa tsirarun da suke zaune a yankin Idiape da Okelele wadanda suka yi kaura daga daular Oyo. A kokarin da malam Ana danganta asalin kafuwarmasarautar Ilorin da zuwan Fulani garin Ilori a bisaniyyasu ta yin jihadin yada addinin Musulunci a wajajen karni na sha takwas zuwa karni na sha tarawadanda suka yi kaura daga Sakkwato a karkashinjagorancin malam Alimi. Kafn zuwan Fulani Iloriakwai al’ummomi da daban-daban a Ilorin da sukezaune a yankunansu kowannensu kuma yana da nashishugaban.Wadannan al’ummomi kuwa sune Yarbawawadanda a lokacin da malam Alimi ya zo Ilorin Afonjashi ne shugabansu. Sannan akwai al’ummar Gambariwadanda suka hada sa Hausawa da Barebari da Gwarida Nufawa da Kanuri da Fulani.
A lokacin jihadi malam Alimi ya nada sarakunanyaki wadanda aka ba wa shugabannin al’ummai daban-daban na Fulani da Hausawa da Yarbawa ammamusulmai. Yin hakan ne ya haifar da rikici tsakaninAfonja shugaban Yarbawa na wannan lokacin suka yitawaye don nuna rashin jin dadinsu wanda daga bayaaka yi nasara a kan shi da jama’arsa. Har zuwa yanzu‘ya’yan Afonja ne su ne ke riqe da mukamin magajinAreeda Baba Isale a unguwar Idi Epe a masarautarIlori.
Shugabannin al’ummomin nan na Hausawa wadandamalam Bako yake shugabanta da na Kanuri da Goborawa suke karkashin malam Tahir ko a kira shi da Solagberu da na Fulani a karkashin Hinna Kunno da kuma al’ummar Yarbawa da suke qarkashin Se’eni da Malam Usman. Wannan shugabanni kuma sun bukacimalam Alili ya zama sarkin Ilorin a farko amma saimalam Alimi ya nuna cewar shi jihadi ne ya kawo shiamma shi maimakon haka sai a ya aika dansaAbdussalami ya zo daga Sakkwato ya zama sarkin Iloria farkon shekara 1816. Malam Alimi ya rasu a shekarar1816

