Home Labarai Harin ECOWAS Kan Nijar ba talaka zai Shafa ba, cewar Abdul’aziz Abdul’aziz Mataimaki na Mus a mman ga Shugaban Kasa Tinubu

Harin ECOWAS Kan Nijar ba talaka zai Shafa ba, cewar Abdul’aziz Abdul’aziz Mataimaki na Mus a mman ga Shugaban Kasa Tinubu

by masta


-“Har Yanzu Ƙofar Tattaunawa A Buɗe Ta Ke, Sai In Ta Citura Ne ECOWAS Za Ta Kai Farmaki, Kuma Farmakin Ba Talakawa Zai Shafa Ba Sojojin Juyin Mulkin Za A Fatattaka”. – Abdulaziz Abdulaziz

Hadimin shugaban ƙasar Nageriya kan harkokin sadarwa, Malam Abdul’aziz-Abdul’aziz ya yi warwarar zare da abawa dangane da batun farmakin da ƙungiyar ECOWAS ke shirin kaiwa ƙasar Niger domin fatattakar sojojin juyin mulkin ƙasar.

Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta jiyo hadimin na shugaban ƙasar ya na bayyana cewa har yanzu ƙofar tattaunawa a buɗe take da sojawan juyin mulkin, ba wai farmaki ECOWAS za ta kai ƙasar Niger kaitsaye ba, kuma ko da kai farmakin ya kama harin ba zai shafi talakawa ba, iya sojawan juyin mulkin za a fatattaka.

“Ko a jiya Malaman addinin musulunci na Nageriya sun kaiwa shugaban ƙasa Bola Tinubu ziyara fadar shugaban ƙasa, sun nemi ya ba su dama su shiga lamarin tattaunawar samar da sulhun, kuma shugaban ƙasa ya ba su dama, nan da gobe ko jibi za su je Niger ɗin domin tattaunawa da sojawan juyin mulkin don ganin an sulhunta batare da yaƙi ba”. In ji shi.

Abdul’aziz-Abdul’aziz ya kuma ƙara da cewa sai in har sulhu ya gagara ne tukun za a kai ga batun farmaki domin zuwa yanzu cewa aka yi dakarun shirin kotakwana na ECOWAS su yi shirin kotakwana ba wai cewa aka yi su afka ba, sai ina ta citura.

“Batu ne na ƴan’uwantaka, ba wai yaƙi ne tsakanin Niger da Nageriya ko da ƙungiyar ECOWAS ba, shi isa har yanzu ƙofar sulhu ta ke buɗe, ana cigaba da tattaunawa, sai in har ta citura ne tukun za a tsala bulala akan sojawan juyin mulkin ba wai talakawan ƙasar Niger ba”. Cewarsa.

Ya kuma ƙara da cewa: “Domin sojawan su ne su ka ƙwace mulki ta ƙarfi su ke neman jefa Niger koma baya ta faɗa irin halin da ƙasashe irin su Mali da Burkina Faso su ka faɗa, dan haka in ta kama a kai farmaki su kaɗai za a farmaka domin tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa ke doka”. Cewar Abdul’aziz-Abdul’aziz, hadimi na musamman ga shugaban Nageriya, kana kuma shugaban ƙungiyar ECOWAS, Asiwaju Bola Tinubu.

Related Posts

Leave a Comment