Home Labarai BA YAU ECOWAS TA FARA BA

BA YAU ECOWAS TA FARA BA

by masta


Wannam rubutun na da tsayi amma zan fi so matasa su daure su karanta shi don kamar sun fi bukatarsa.

Halin da ake ciki a Kasar Nijar sakamakon juyin Mulkin Soji ya ja hankalin duniya musamman ma bayan shigowar ECOWAS da dibar wa’adin kwanaki 7 da tayi na sojojin su mai da mulki ko ta far musu.

Wannan lamarin ya haifar da tsoro, tausayi, fargaba ga makomar wannan yanayi idan ya rikide zuwa yaki. Sai dai abin tambaya anan shine Shin Me ya bai wa ECOWAS karfin gwiwar iya daukar wannan matsaya? Wasu zasu ce watakil yawan mambobi da karfin tattalin arzikin Kungiyar ne ke dibanta yayinda dattijai irin mu mun fi alakanta hakan da nasarorin da kungiyar ta samu a matakanta da ta sha dauka a baya. Don haka ne na ga ya kamata mu yi waiwaye adon tafiya mu ga me ECOWAS ta yi baya?

-1990
A shekarar 1990 kungiyar ta raya tattalin arzikin yankin Africa ta yamma wato ECOWAS ta haifi wata kungiyar wadda aikinta shine samar da wasu sojojin kawance na musamman a tsakanin Mambobin kungiyar da za su rika dakile duk wani hura hanci da aka iya samu a cikin kasashen kungiyar, kama daga juyin mulki, yakin basasa, kutse da dai sauransu

LIBERIA
Ai kuwa daga kirkirarsu dama aikin yi na jiransu inda a shekarar ake fama da tashin hankali a kasar Liberia karkashin CharlesTaylor wanda daga juyin mulki ya rikide zuwa yakin basasa. Saidai Sojojin na ECOMOG dubu uku karkashin Amara kirjin biki wato Hana-biki-maraici Najeriya suka je suka daidaita al’amura suka dawo da kwanciyar hankali a kasar duk da sun bar baya da kura domin sun yi zaman dirshan a kasar har shekaru 6 wanda ya haifar da cin zarafin ‘yan mata domin ko Najeriya kadai ta dawo da guzirin ‘ya’yan gaba da fatiha da aka ce yanzu haka suna da kungiya ta ‘yan gaba da father Najeriya wajen dubu 12 (Allahu aalamu) amma dai an sami lafiya kuma Najeriya ba ta sami ko kwarzane a yakin ba ta dawo gida har ma ta baiwa manyan dakarun da suka dawo manyan kujeru a cikin gida

1997 Saliyo

Wannan nasara ta fasa kan sojojin na ECOMOG inda a shekarar 1997 Sojoji karkashin Paul Koroma suka kifar da zababbiyar gwamnati a kasar Salo: General Abacha yayi irin ta Shugaba Tinubu inda ya bai wa Sojojin wasu ‘yan kwanaki da su mai da Tejan Kabbah ko su dandana kudarsu. Shi ma Janar Abacha a wancan lokacin ya sha tofin Alatsine daga cikin gida Najeriya inda masu adawa da lamarin ke duba da cewa Shi kansa Abacha soja ne ya kuma kasa mai da Najeriya ga Mulkin DIMUKRADIYYA amma yana kare DIMUKRADIYYAR a wata kasa. Wato dai Daddawa gaya manda baki. Amma haka yayi kunnen uwar shegu inda ya tura sojojin Najeriya suka shiga rigar ECOMOG suka dawo da Malam Kabbah a cikin kwanaki 15 kacal a wancan lokacin ma ba mu fuskanci wata matsala ba a Najeriya domin wasu sojojin Najeriya ne da ke Birnin Monrovia aka umarta da su gangara su shiga Freetown su fatattaki Koroma.da tawagarsa ta RUF Wato Revolutionary United Front wanda su ma a lokacin suna ikirarin ceton kasar ne daga harkallar mulkin mulaka’u.

1999: Guinea Bissau

Can ECOMOG ta cilla a shekarar 1999 a matsayin kwamandar tsagaita wuta bayan rikicin da ya barke sakamakon yunkurin juyin mulkin da ya kasa kai bantensa kasancewar shugaban na samin kulawar sojojin kasar Senegal bayanda duk wani yunkurin sulhun da aka yi a shekarar1998 ya lalace. ECOMOG din ce ta taimaka aka kafa gwamnatin hadin kan kasa a nan Abuja a shekarar 1999 bayan da ta kawo masu gaba da junan shalkwata aka sulhunta

2003 Ivory Coast

A shekarar 2003 kuwa ECOWAS da kanta ta tura sojoji Kwadibuwa bayan da yan tawayen kasar suka amince su jingine makamansu

2003 Liberia 2nd
A wannan lokacin ma baya ta barke, domin kuwa a can Liberia fa Charles Taylor ya dawo har ya tunkuyi gwamnati an soma yakin basasa, kuma idan aka kyale shi ba kawai Liberia zai wa barna ba sai ya jika wa garin ECOWAS ruwa a Saliyo tunda dama shine Uban gidan Fpday Sankoh wanda ya jaza wa Saliyo din bala’i don haka dole a koma a yi Fadan The End da shi. A wannan lokacin dai ECOMOG tayi dogon suma domin Ubanta Abacha ya kwanta dama don haka ne aka tura Wata sabuwar tawagar da sabon suna wato ECOMIL ana nufin Dakarun ECOWAS, nan ma dai karkashin Amara kirjin biki Najeriya inda a wannan karon sai da suka cukwikuyo Charles Taylor suka kawo wa shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo kana suka share fage ga Sojojin wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya UNMIL a kasar wanda nan ma fa NAJERIYA ce me masaukin baki.

2013: Mali

A shekarar 2012 an yi juyin Mulki a kasar Mali wanda ya tsunduma kasar cikin yakin sunkurun da har yau bata warware ba duk da kiranyen da take wa Rasha na neman taimako

A nan ma ECOWAS ta Hubbasa karkashin wata tawagar soji karkashin AFISMA don taimakawa Hukumomin Kasar ta Mali. A wannan lokacin Giwar mata Najeriya na fama da matsalar Boko Haram don haka sunanta bai yi tashen da ya saba ba amma fa ko za a mutu sai an shura, Don haka sojin Najeriyasun fi yawa a awannan tawagar ma, amma anan har Burkina Faso ta tabuka da nata sojin amma fa shiru kake ji

2017: Gambia

Nan kuma Yahya Jameh ne ya nemi gurgunta Dimukradiyya ta hanyar kin Mika mulki ga zababben Shugaban kasr Gambia Barrow adama ta inda sai a embassy din kasar Senegal aka rantsar da shugaban kasar ta Gambia a can kuma ya fara mulki saboda Daurin ture ka ga tsiyar da Jameh ya nada a fadar Gambia. Sai dai a kwana uku ECOWAS ta fatattaki Yahya inda ta nuna masa shiru-shiru fa ba tsoro bane gudun magana ne.

2021-3 Mali da Burkina da Guinea

A cikin shekaru uku kasashe uku Mambobin wannan kungiya sun yi juyin Mulki amma ECOWAS bata yi abin azo a gani ba sai takunkumin da ta sanya musu shin ko menene ya janyo wannan sakacin wanda kuma a yanzu da alamar ECOWAS na so ta dawo da martabarta ta a kan Juyin mulkin Nijar?

Shine abin da zamu kalla idan Mai bayar da saa ya bamu.

Amma kafin nan ya kamata mu sani
Cewa ba kamar yadda Mutane ke tsorata ba ko a yake-yaken baya da Najeriya ta shiga bata janyo yakin da zai cutar da yan kasarta, saboda ba da ilahirin sojin kasa take yaki ba da ‘yan tawaye ta kan yi kuma ba wai bata fuskantar matsalolin cikin gida bane a lokutan baya. Kawai dai da ruwan ciki ake jan na rijiya take yi. Kazalika a yakin ta kan sami wasu nasarori na cikin gida,
Misali daya daga cikin nasarar da Najeriya ta jima ta na samu a yakunan kasashen Saliyo da Laberia shine shagalar da sojojinta daga matsalolin mulki na cikin gida inda sukan sami aikin yi a wadancan kasashen su shagala da su. Misali a Liberia Najeriya ta jima tana jan akalar sojin kasar har ma ta sami wata kujera da kadan ta kusa fin ta shugaban kasa mai suna 1st Commander a Kasar Liberia wanda a kan baiwa General din Najeriya ne, kamar yadda muka dade muna rike kujerar Chief Of staff a Saliyo. Baya da wannan Sojojin Najeriya na sami. Kwarewa a fagen daga da kuma samin kayan yaki musamman yayin wanzar da zaman lafiya karkashin majalisar dinkin duniya inda sukan cakudu da takwarorinsu na kasashen duniya masu tarihin karfin soja irinsu India Pakistan da sauransu.

Idan har kun iya karance wannan rubutun zaku gane dalilin ECOWAS na jin zata iya wannan bikin da ta debo.

Rahama Abdulmajid

Related Posts

Leave a Comment