
A ranar laraba 2 ga watan Agusta 2023 Al’ummar da suka cika ciki da wajen harabar gidan Murtala da ke Kano kadai ta isa Shaidar cewa wa ne sheikh Tijjani Sani Auwalu. Bayan shehu Tijjani ya shiga Ofis ne aka yi addu’oi na Neman nasara da kariya daga nan sai Shehu Tijjani ya yi takaitaccen bayani kan Tarihin wannan ofishi na Addinai da zai shugabanta a Matsayin kwamishina sannan kuma ya Kara jaddada manufar kafa wannan ofishi ita ce Samar da hadin Kai Tsakanin dukkan Addinai don haka ofishinsa ba ruwansa da kowanne bangaranci ofishi ne na adalci tsakanin kowacce akida da kowanne addini. Sannan Kwamishinan ya yi Kira da al’umma kan duk lokacin da suka ga wani abu da ya dace a nusar da al’umma ko Wani Abu da yake bukatar Jan hankalin gwamnati ko shawara su gaggauta Sanar da odishin ta hanyoyin da ya dace saboda kofar ofishin a bude take tana bukatar a yi komai a tare don cigaban jihar Kano. Kwamishinan ya kuma cewa Ofishinsa ofis ne na aikin al’umma don haka yana maraba da Wanda ya zo taimaka masa a kan aikin amma kuma in har batun zumunci ko hira ko akida to wannan a jira a gida ko wuri na musamman. Batun juriya da hidimar jama’a Shehu Tijjani ya ya fadi cewa in har Ana gado to ya yi don mahaifinsa ya karar da rayuwarsa ne wurin yi wa addinin Musulunci hidima a ciki da wajen Nijeriya kasashen nan na Afrika ba inda bai taka ba don yada addinin Musulunci haka mahaifiyarsa ta koyar a mataki daban-daban a kasar nan don haka hidimar addini wannan gado ne kuma zai dora ba tare da gajiya ko kosawa ba. Zai tabbatar da komai an ajiye shi a gurbinsa. A karshe Kwamishinan ya ce shi da ofishinsa na Kano ne Baki daya ,ba iya karamar hukumar Kumbotso ba. Ya yi godiya da fatan alheri ga duk wandanda suka bar ayyukansu suka zo don shaida wannan rana” Shi ma mai gayya me aiki Dr Ali Tamasi ya yi godiya ga Allah ga duk Wanda ya halarci wannan muhimmiyar rana sannan ya jaddada godiyarsa ga jagoran Kwankwasiyya Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf kan wannan kujera ta Kwamishinan Addinai lallai an yi abin da ya dace. A karshe Dr Tamasi ya yi godiya da fatan alheri ga dukkan Wadanda suka halarci wannan rakiya sannan ya yi Addu’ar Allah ya dafawa Kwamishinan ya yi riko da hannayensa Amin.
Yadda Shehu Tijjani ya Shiga Ofis a Matsayin Sabon Kwamishinan Addinai na Jihar Kano.
572

