Home Labarai Bola Tinubu: AREWA SAI GODIYA

Bola Tinubu: AREWA SAI GODIYA

by masta


AlhamdulilLahi ya zuwa yanzu a ɓangaren ɗane-ɗanen muƙaman gwamnati Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna bai manta da kara da halarcin da mutanenmu na Arewa suka yi masa ba a lokacin zaɓe.

A cikin kammalallen list na sunayen ministoci ƙididdiga ta nuna cewa Arewa ke da kaso mafi rinjaye (guda 26) a cikin sunayen mutane 47 da za a naɗa ministoci. Arewa-maso-Yamma ita tafi ko ina yawan ministoci (10) domin kuwa shugaban ƙasa ya bada ministoci bibiyu daga jihohin Katsina, Kano da Kebbi. Arewa-maso-Gabas tana da 8 sai Arewa ta tsakiya da take da takwas ita ma.

Fatanmu shi ne Allah ya sa waɗannan mutane bada kyakkyawan wakilci tare da riƙewa shugaban ƙasa amanar jama’a.

Ba ya ga ministoci shugaban ƙasa ya naɗa ko kuma ya cigaba da aiki da waɗannan ƴan Arewa a manyan muƙamai: 1. NSA
2. Chief of Defence Staff
3. Chief of Air Staff
4. Director General DSS
5. Director General NIA
6. GMD of NNPC

Da sauran wasu da dama da suka haɗa da Special Advisers da manyan mataimaka (SSAs).

Ko yanzu shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba maras ɗa kunya. Su kuma waɗannan manyan jami’ai Allah ya sa kada su bawa shugaban ƙasa da al’ummar mu kunya. Amin!

Related Posts

Leave a Comment