
APC A YAU
Daga
Bilkisu Yusuf Ali
wamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, a ranar Talata ya rantsar da kwamishinoni da masu bashi shawara ta musamman su 38 da za su kasance ‘yan majalisar zartarwar jihar.
A bikin rantsuwar da ya gudana a filin taro na ‘Peoples’ Square, Katsina, an rantsar da kwamishinoni 20 da masu ba Gwamna shawara ta musamman su 18.
A jawabin Malam Dikko Umaru Radda PhD, ya hori wadanda aka rantsar din da su sani cewa amana ce aka damka musu, don haka suke da bukatar su tsare ta kamar yadda Allah Ya bukata.
Gwamnan na jihar Katsina ya tabbatar musu da cewa ba zai bar kwamishina ya dawwama a ma’aikata daya ba, zai rika sassauya su lokaci bayan lokaci daga wannan ma’aikata zuwa waccan don jihar Katsina ta amfana da dumbin ilmi da basirar da Allah Ya huwace musu.
Ya hore su da cewa, duk wanda aka nada mukamin, al’ummarsa ne suka zabo shi, domin suna da amannar cewa zai ba su gudunmuwa yadda ya kamata, don haka, akwai bukatar su yi damarar sauke nauyin al’ummarsu yadda ya dace.
Malam Dikko Umaru Radda ya ja hankalinsu da kwange wajen zuwa aiki ko zuwa makare. Inda ya kara da cewa gwamnatinsa za ta rika bibiyar dukkanin ayyukan wanda aka ba amanar wani wuri don gudun ‘cin tuwo da miyar bara’.
Malam Dikko Umaru Radda PhD ya sanar cewa gwamnatinsa na shiri na musamman domin fito da hanyoyin samar da tallafin da zai rage radadin cire tallafin man fetur da ake ciki.
Ta fuskar tsaro kuwa, Malam Dikko Radda ya ce gwamnatinsa ta gaza zaune ta gaza tsaye, wajen ganin ta samo hanyoyin da mutanen jihar Katsina za su zauna lafiya a yankunansu, musamman karkara.
SSA Isah Miqdad,
1/8/2023.

