Home Labarai Dr Dikko Radda ya Umarci a gaggauta biyan diyyar wadanda aikin fadada filin jirgin Sama ya shafa

Dr Dikko Radda ya Umarci a gaggauta biyan diyyar wadanda aikin fadada filin jirgin Sama ya shafa

by masta

Malam Dikko Radda ya umurci a gaggauta biyan diyya ga wadanda aikin fadada filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua, Katsina ya shafa . Gwamna Dikko Radda PhD ya umurci da a gaggauta biyan diyya ga mutanen da aikin fadada filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua, Katsina ya shafa da gwamnatin tarayya ke gudanarwa.

Gwamnan ya sanar da hakan a lokacin da ya ziyarci babban Sakatare a ma’aikatar sufurin jiragen sama Dr Emmanuel Meribole a ranar Juma’a 21st Juli, 2023 a ma’aikatar, Abuja.

Malam Dikko Umaru Radda ya ce tuni ya umurci da a fitar da kudade domin biyan diyya ga masu filaye da gonakin da aikin fadada filin jirgin zai shafa ba tare da bata lokaci ba domin samun damar fara aikin cikin kankanin lokaci.

Gwamnan ya yi godiya ga tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari da tsohon ministan sufuri Sanata Hadi Sirika bisa yadda suka yi aiki kasa-rika don inganta filin jirgin sama na Malam Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina ya shiga tsara a idon duniya.

Gwamna Radda ya yi godiya sosai ga ma’aikatar sufurin jiragen sama da ta tsara gudanar da wannan aiki a filin jirgin sama na Katsina, inda ya ce Katsinawa sun dade su na mafarkin samun irin wannan cigaba, ga shi yanzu mafarkinsu ya zamo gaskiya.

A nasa bangaren, Babban Sakatare a ma’aikatar sufurin jiragen sama ta Nijeriya Dr Emmanuel Meribole ya taya murna ga Malam Dikko Umaru Radda bisa nasarar zama Gwamnan jihar Katsina. Ya kuma yi jinjina ga matakin Gwamnan na umurtar a gaggauta biyan diyya ga wadanda aikin zai shafi kadarorinsu domin aikin ya soma cikin lokaci.

Idan za a iya tunawa dai, gwamnatin tsohon Gwamna Masari, ta ba da fili domin fadada filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua, Katsina. Aikin da zai lakume bilyoyin kudi, na da nufin kafa sassa hudu da suka jibinci filin jirgi da ake kyautata zaton kammala aikin cikin watanni 12. Idan an kammala aikin, zai samar da ayyukan yi ga Katsinawa kusan 1,500.

SSA Isah Miqdad,
Ofishin Daraktan Yada Labarai,
21/7/2023.

Related Posts

Leave a Comment