A yau 24/7/2023 shehi Tijjani Sani Auwalu daya daga cikin kwamishinonin da Maigirma Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya zaba don rike ofishin addinai na jihar Kano ya bayyana a gaban majalisa don tantance shi. Bayan shehi Tijjani ya gabatar da Kansa babban abin da ya dauki hankalin yan majalisa shi ne Shehu fa international Shehi ne ya Saba da hidimar addini hasali ma Gidansu hidimar ya gada. Don haka suka fara yabawa da kuma ba da shawarwari kan muhimman mas’aloli da suka dami Kanon musamman ta hadin kan Al’ummar jihar Kano kan Bambamcin akidu da masu sakin Baki yayin waazi da kuma matsalalin bara a Kano. Shehu Tijjani ya ba su amsa inda ya fara fada musu zai yi iyakar iyawarsa kan ya ga ya yi adalci a duka Tsakanin kumgiyoyin darika da muke da su a Kano sannan batun waazi zai yi duk me yiwuwa kan ya ga ba a Samu sakin Baki ba In ta Kama a Samar da lasin na waazi za a yi don dai a tabbatar an yi abin da ya dace. Batun bara da Almajir ci nan ma shehu ya fada musu za a yi komai cikin tsari inda za a tabbatar da kowanne tsarin Ilimi na tsangaya da na Zaure da na Islamiyya kowanne na nan amma cikin tsari sannan ita kanta barar za a duba mene yake kawota don a nemi mafita. A karshe Kwamishinan ya yi godiya tare da rokon bude masa kofa kan koyaushe ya zo da Neman shawara Yan majalisa su amince. Ga dukkan me ba da shawara Nan ma ya ce yana maraba wannan ofishi na al’umma ne nasarar aikin yana hannun al’umma ta yarda suka bayar da hadin Kai da goyon baya. Haka yana rokon gwamnatin Kano da ta ba wa ofishin goyon baya don samun cikakkiyar nasara . Hakika Jawaban Kwamishinan ya ratsa jikin mutane kan lallai Hausawa sun yi gaskiya Cewar da mai Kama ake kota!
Shehi Tijjani Sani Auwalu da Kyawawan Manifofinsa a gaban Majalisar jihar Kano
561


