287
Abba El-Mustapha ya karbi takardar nadin da Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya yi masa a matsayin Babban Sakatare na Hukumar Tace Fina-finai da dab’i ta Jihar Kano daga Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Dr Abdullahi Baffa Bichi. Gwamna Abba ya naɗa El-Mustapha ne a matsayin Babban Sakataren Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar duba da cancantarsa da kwazonsa. Sakataren gwamnatin ya mikawa Abbba takardar ne a madadin Gwamnan na jihar Kano. An dai jiyo abokanan sana’ar ta Abba suna murna da fadin lallai an yi hange da aka ba wa Abba wannan kujera don ya dace da ita.Bilkisu Yusuf Ali
22/7/2023


