Yayin zagayen ziyara da MD Karota ya yi atashoshin Mota yan Tashar Rijiyar zaki sun Mika manyan kokensu na abin da ke ci musu tuwo a kwarya na abin da gwamnatin baya ta jihar Kano ta yi musu a tashar. Yan tashar sun ce bayan gine-gine da aka yi aka cushe tashar da shaguna da gidaje inda har ta Kai motocin da aka yi tashar dominsu ba su da wuri. Sannan kuma suna rokar Shugaban na Karota da ya dawo da masu Lodi akan Gadar Kabuga cikin Tasha don Habaka tashar. Maigirma MD ya ji kokensu kuma ya yi musu alkawarin dawo da Martabar ta tashar Rijiyar Zaki sannan ya jaddada musu yunkurin tsohon Gwamnan na jihar Kano Injiya Rabiu Musa Kwankwaso na samar da tashar da ingantata ba zai zama a banza ba suna za su d’ora daga inda ya tsaya kuma ba za su bar kowanne irin zalunci ba. Sannan Maigirma MD ya kuma jaddada kudir da fata na Gari da Maigirma Gwamnan Kano yake da shi ga Kanawa Wanda yake da tabbacin Kanawa Sun yi dace da gwamna na Gari me hangen nesa.

Ziyarar MD Karota Injiniya Faisal Tashar Rijiyar Zaki sun Mika Kokensu
436

