
Tsadar Rayuwa Da Tsadar Man Fetur A Nageriya: Wa Ke Da Laifi Tsakanin Sabuwar Gwamnatin Tinubu Da Tsohuwar Gwamnatin Buhari ?
DAGA Bashir Abdullahi El-bash
Ƴan Nageriya da dama na ɗora laifin matsalar da ake ciki ta tsadar man fetur da rayuwa akan sabuwar gwamnati ta shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Sai dai abin da ya kamata jama’a su fahimta shi ne, har yanzu Bola Tinubu bai yi kwana 100 akan mulki ba. Bai naɗa ministoci da sauran jami’an gwamnati ba.
Tinubu har yanzu da tsofin ƙusoshin gwamnatin Buhari ya ke aiki, kamar misali shugaban kamfanin man fetur na ƙasa NNPC, Mele Kyari, Buhari ne ya gadarwa Tinubu shi.
Hatta tallafin man fetur Buhari ya taɓa faɗa kafin ya bar mulki cewa sun tsara yadda gwamnati mai zuwa za ta cire shi.
Ko da kasafin kuɗi Tinubu bai tsara nasa ba, ya na amfani ne da na 2023 wanda tsohuwar gwamnatin Buhari ta tsara.
Kenan akwai buƙatar ƴan Nageriya su cigaba da addu’a, su ba wa shugaban ƙasa Tinubu lokaci, su jira ya naɗa ministoci da sauran jami’an gwamnati ya yi kasafin kuɗinsa gwamnatin ta zauna da gindinta kafin ɗora masa alhakin matsalolin da ba shi ne ya kar zomon ba, ratayarsa aka ba shi.

