Home Labarai Ya kamata Maza ku daina rudar Kan ku da Karin Maganar Duk Abin da Namiji ya yi Ado ne.

Ya kamata Maza ku daina rudar Kan ku da Karin Maganar Duk Abin da Namiji ya yi Ado ne.

by masta

A kowanne lokaci al’umma na kallon shi namiji da tsarkin da ya fi mace ko kuma wanda shi laifi ba ya bin sa komeya yi zai wuce.Wannan fahimtar ta rudi maza da damasannan tana ci wa mata tuwo a kwarya ya za a yi su aika

laifi iri guda amma al’umma ta hukunta wanibangaren ta kau da kallonta a wani sashen.Abin hakayake sai dai a yau zamani ya fara yi wa maza hukuncisun daina cin bulus a kan laifi.Laifi ya bi mata wannantsohon gado ne da yake bin mata tun daga lokacinMaguzanci inda ake bin diddigi kan matar da ba ta kaibudurcinta ba dakin miji.Akwai tsafin da za a yi idanmace ba ta kai budurci ba za ta mutu nan take.A wanitsafin kuwa za a hada ta da dan kwikwiyo wanda za ta yi ta yawo da shi tsahon rayuwarta wanda wannanshaida ce na al’umma su ga abinda ta aikata.Shi kuwanamijin da suka aikata laifin tare ba a ko nemansa kodakuwa in an neme shi zai musa.Amma me yasa aka fi ganin laifin mace.

To amma maza su sani a yau, su ma maza wannan adonda ake ambata musu ya gushe ya sauya salo yayin da suka aikata wani abu marar kyau yana bin su don hakaya kamata iyaye su cire wannan Karin maganar a bakunansu lokacin da suke yi wa yaronsu nasiha. Ba inda mummunan aiki yake zama ado kawai don ya zo a namiji.Da dama mutum zai je neman aiki ko zai zohawa wani muqami a tado ire-iren munanan ayyukanda ya aikata da a lokacin ake kallonsa. Misali kalliyadda ake yi wa ‘yan siyasa ko wani fitacce A kwanannan wani ya xaura xamarar fitowa takarar wata babbarkujera ashe a baya ya tava haihuwar yarinya kafin auredon haka aka lalubo yarinyar aka yaqi takarar da itayana ji yana gani gudun sharrin ban ji ba ban gani baya haqura ya ajiye takarar. Ba abin da ya fi mutunci a yau ya kamata maza su yi takatsan-tsan su san yayinda suke yin wani abu , a yau da duniya ke tafin hannulokaci na yanar gizo da kafofin sadarwa iri-iri to fa ba za su sha ba kamar yadda yake a baya a kan mace idan ta aikata abu zai shafi iyaye da iyalai a yau akanmazan ma haka ne don haka maza a kiyaye a watsar da karin maganar nan ta DUK ABIN DA NAMIJI YA YI ADO NE

Related Posts

Leave a Comment