Home Labarai Sarkin Kano Marigayi Alhaji Ado Bayero tarihinsa da Gwagwarmayar Rayuwa

Sarkin Kano Marigayi Alhaji Ado Bayero tarihinsa da Gwagwarmayar Rayuwa

by masta

Lafiya ci-gari uban Gabasawa magajin Abdullahi Dabo,

Lafiya Amalen Sarakuna

Lafiya Dagi maganin Kasa mai tauri

Lafiya Hadarin Kasa maganin mai kabido

Lafiya sarkin yakin sarkin Musulmi

Gaba Salamun baya salamun toron giwa ka dade.

Rugum Babban Motsi!

Bayan goyon marayu , mai uban ma kai ne Babansa, kuma jigon Kanawa namiji sannan jarumin gaske! Marigayi Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero. Tarihin Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da ci gaban da ya kawo ba zai taba yi wuwa a kawo shi ba a zama daya sai dai a kawo abin da zai samu don Bahaushe ya ce abin da yawa mutuwa ta shiga kasuwa.

Tarihinsa

An haifi mai martaba margayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ranar 15 ga watan Yuli 1930 a unguwar Bare-bari da ke gidan Sarki. Mahafiyarsa sunanta Hajiya Hasiya (Mai babban daki).Yaya Maimuna da Yaya Kubra ne suka dauki renonsa a a 1937. An mayar da rainonsa wajen Maikano Zagi inda ya ci gaba da rayuwarsa hannunsa har sai da aka yi masa aure.

Karatunsa

Sarki Ado ya fara karatun allo ne a tsakanin 1934 zuwa 1938 da ilmn Elemantire ya fara karatu a makarantar kofar Kudu da ke gidan sarki daga 1938-1942. Daga nan ya zarce makarantar midil wadda yanzu ake kira da Rumfa College daga 1942-1947 daga 11947 zuwa 1949 sai ya tafi makarantar koyon shari’a wadda yanzu ake kira da makarantar S.AS. Daga nan ya tafi makarantar koyon akawu . A 1951 An yi wa Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero auren fari.A 1952 kuma ya je Karin ilimi a makarantar koyon gudanar da mulki da ke Kongo a Zaria

Gwagwarmayar Rayuwa

Mai martaba San Kano ya yi aikin Bankin Biritish (British Bank) wanda a yanzu ya kom first bank. A shekarar 1956 ya tafi jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria ya yi kwas a bangaren koyon akin mulki a shekarar 1957 ya shiga majalisar wakilai ta arewa. A tsakanin 1958-1962 ya yi wakilin ‘yan doka a yankin mulkin Kano gaba daya. Kuma a shekarar 1962 ya halarci wani kwas na koyon ayyukan shari’a da bincike da suka shafi ‘yan doka. Ya y kwas din dansandan ciki a Scotland a kasar Ingila. A 1962 ya zama jakadan Najeriya a Senegal Ya halarci Kwas din koyon harshen Faransanci a kasar Switzerland. Ya zama Sarkin Kano a shekarar 1963. Inda ya zama sarki na goma sha uku a tsarin sarautar Fulani.

Zamansa Sarkin Kano

Bayan Rasuwar Sarkin Kano Muhammadu Inuwa da Kwana daya sai Razdan (Baturen mulkin mallaka) na Kano na wancan lokacin mai suna St. E.D Nelson ya aiko yana neman masu zaben sarki. Bayan duk an bi dabaru da sharuddan zaben sarki sannan da irin gudummawar da ya bayar kamar wajen hadin kan jama’a da samar da zaman lafiya a Kano lokacin da yake Danmajalisa a Kaduna. Haka kuma sun yi la’akari da kwazonsa da kyawawan halayensa lokacin da yake wakilin doka. Sun kuma yarda da cewa halayyarsa da jama’a ta kirkice kuma abar girmamawa, sannan yana da haba-haba da kowa ga rashin girman kai. Daga nan ‘yan majalisar zaben sarkin Kano suka gaya wa Mr Nelson wanda suka zaba tare da dalilansu.

Mr Nelson ne ya bayar da sanarwar gwamnatin iahar Arewa ta yarda da zaben Alhaji Ado Bayero ya zama sarkin Kano. Tun daga wannan rana shi ne wanda ya ba wa sarautar Kano.

Wasu Daga Cikin Ayyukan Mai martaba Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero

Akwai ayyukan Bunkasa kasa. Alhaji Ado ya nuna gwazo kwarai da gaske wajen kyautata kasar nan baki daya. Ya zama Shugaban majalisar Gudanarwar jami’ar Nsuka daga shekarar 1966-1976. Haka kuma ya taba zama shugaban jami’ar Ibadan da kuma Maiduguri ashkarar 1988 har ila yau ya taba zama mataimakin shugaba na hukumar jami’oin duniya a shekarar 1978. A bisa al’ada takan hadu ne a kalla sau 3 a shekara domin tattaunawa kan matsaloln da jami’oin kan fuskanta. Ita ce mai kula da dukkan al’amuran da jami’ar ke gudanarwa. Sarki Ado ya taba zama wakili a majalisar sarakuna ta Arewa. Haka kuma shi ne mataimaki na biyu a tsarin shugabancin Jama’atu nasaril islam. Qungiyar da ke tallafawa addinin muslunci ta fuskoki daban-daban. Ya riqe muqamin jagoran mahajjata a Najeriya Amirul Hajj a shekarar 1994.

A jerin sarakunan Kano ba a sami sarkin da Allah ya bai wa lafiya kuma ya yi amfani da llafiyarsa wajen daukaka addinin Allah kamar sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ba. Sam ba ya gajiya wa wajen qaddamar da ginin masallaci ko bude shi ko gina makarantar islamiyya ko kuma saukar karatun alkur’ani mai girma. A cikin shekara daya tsakanin 1998-1999 sarki ya bude masallatai na juma’a guda dari uku bayan wanda bincike ya gaza samo su. Sannan ya yi limancin bude su. Haka ma makarantun islamiyya ba za a iya kididdige su ba. A kididdiga a tsakanin 1998-2013 ana iya has ashen mai martaba Sarkin Kano ya bude masallaci dubu hudu da dari biyu masu hasashe suna ganin kidddigar ta fi haka nesa ba kusa ba saboda Kano kullum dada bunkasa take.

A bangaren samar da zaman lafiya kuwa mai martaba sarkin Kano ya yi zarra a wannan fagen misali samar da zaman lafiya a lokacin da aka yi vararren juyin mulki da aka kashe Shugaban Qasa Murtala Ramat Muhammad a shekarar 1975. Shugaban qasa kuma haifaffen Kano. A lokacin an ta yada jawaban mai martaba Sarkin Kano na kwantar da hankalin al’umma har sai da ya tabbatar kome ya lafa. A shekarar 1976 an dauki matakai da dama a tsakanin masu fada a ji da wasu kungiyoyin Yarbawa domin sasanta wata ‘yar hatsaniya da ta tashi a tsakanin wasu sarakunan Yarbawa guda biyu wato Alafen Na Oyo , Oba Lamidi Olayiwal Adeyemi da Shoun na Ogbomosho Oba Oladunmi Oyewunmi Aja Ogungba wanda shugaban yarbawa suka yi abin ya ci tura. Sai da Shugabannin Yarbawa suka yi wa mai martaba gayyata ta musamman domin ya shiga cikin maganar kuma ya nuna wa kowa kuskurensa daga nan ba a kuma sake samun rashin jituwa a tsakaninsu ba.

Mai martaba Sarkin Kano ya yi namijin kokari wajen samar da zaman lafiya tsakanin kiristoci mazauna Kano. Duk ana zaune lafiya da juna.

Duk wanda bai kalli hawan Sarki Ado ba to tabbas yana da sauran kallo. Domin kuwa ba sarkin da ya kai Mai martaba sarkin Kano. Akwai hawan Idi da Hawan Daushe da Hawan Nassarawa da Hawan Dorayi ko Fanisau. Duk wannan hawan da Mai martaba yake yi hawa ne na kallo da kwalliya da Kasaita wanda ba zaka taba ganinsa a kowane wuri ba sai Kano. Lallai Kano ta zama Jalla babbar Hausa Yar ko da mai ka zo an fi ka.

Rasuwarsa

Marigayi sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya rasu ranar Juma’a 6 ga watan Yunin shekara ta 2014 yana da shekara 84 a duniya. Ya bar matan aure 4 da kwarkwarori 16 da ‘ya’ya 61 da jikoki sama da 300. Allah ya jiqansa da gafara ya albarkaci zuri’arsa.

An sami wani sashe na wannan hirar ne a cikin littafin Awa Ashirin da hudu a gidan Dabo tare da sarkin Kano Alh Ado Bayero. Na Rabi Talle Maifata.

Related Posts

Leave a Comment