Home Labarai Sakon Sabuwar Shekarar Musulunci daga Shugaban Kasa Alh Bola Ahmad Tinubu

Sakon Sabuwar Shekarar Musulunci daga Shugaban Kasa Alh Bola Ahmad Tinubu

by masta


Ina amfani da wannan dama domin taya Musulmin Najeriya da na duniya baki daya murnar Sabuwar Shekara.

Ina addu’ar Allah Ya sa wannan shekarar da muka shiga ta 1445 bayan Hijirah ta zo mana da alheri da zaman lafiya da cigaba mai dorewa da aminci.

A lokacin da muke murnar shiga Sabuwar Shekarar nan, ina kira ga ‘yan Najeriya da su kasance masu hakuri da juriya da imani da kaddara kamar yadda Hijirar Annabi Muhammad (S.A.W) daga Makka zuwa Madina a shekara 1445 da suka gabata ta koyar.

A daidai lokacin da muke ta kokarin fuskantar kalubalen da ke gabanmu da tsananin da muke fuskanta, wanda nake da yakinin cewa na wani dan lokaci ne, ina kira ga ‘yan Najeriya da su kasance masu fatan alheri da yakinin cewa lallai gaba za ta fi baya kyau da albarka.

Ni da mataimakana ba za mu huta ba face mun tabbatar da mun cika alkawuran da muka dauka wa ‘yan Najeriya duk kuwa da matsalolin da muke fuskanta a yanzu.

A wannan lokaci da muka shiga Sabuwar Shekara ta Musulunci, ina kira gare ku da ku kasance masu addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da Ya kawo mana dauki, Ya wanzar mana da zaman lafiya da cigaba a Najeriya.

Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Kasa

Related Posts

Leave a Comment