314

A yau Laraba 19 July 2023 MD na hukumar KAROTA Injiniya Faisal Kumbotso ya kai ziyara manyan tashoshin mota da ke Mariri da Na’ibawa da Tashar ‘Yankaba da ta Unguwa Uku. MD din Karotar ya Kai wannan ziyarar ne don ganawa da al’umma da sabunta zumuncin aiki Tsakanin jami’ansa na Karota da direbobi domin Tsaftace harkar sufuri don inganta Lafiyar al’ummar jihar Kano.

