Home Labarai Fatan Alheri da Taya Murnar shiga Sabuwar Shekara ga Al’ummar jihar Kano daga Kwamishinan Addinai

Fatan Alheri da Taya Murnar shiga Sabuwar Shekara ga Al’ummar jihar Kano daga Kwamishinan Addinai

by masta

Tare da
Bilkisu Yusuf Ali

Kwamishinan addinai na jihar Kano Sheikh Tijjani Sani Auwalu Yana yi wa Al’ummar Musulmi na Jihar Barka da Shigowa Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1445 bayan Hijirar Annabi Muhammad (S.A.W). Tare da yin fatan alheri. Kwamishinan Ya yi Kira ga Dukkan Al’ummar Jihar Kano da su yi Addu’ar samun zaman lafiya da Samun Saukin rayuwa a cikin wannan Sabuwar shekarar da muka shiga. Sannan a yi wa Shugabannin na kasa da na jiha Musamman Maigirma Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf addua da nuna cikakken goyon baya don ba shi kwarin gwiwar sauke nauyi da cika alkawuran da ya dauka.

Allah ya karawa jihar mu ta Kano albarka Allah zaunar da mu lafiya da karuwar Arziki Amin Na gode.

Related Posts

Leave a Comment