Home Labarai Wa ya San Gobe?

Wa ya San Gobe?

by masta

Fadakarwa
Tare da
Yasir Kalla

Misis Victoria Gowon ta kasance ɗalibar koyon aikin jinya a asibitin University College Hospital, Ibadan (UCH).

Wata rana rashin lafiya ta kama ta a yayin da suke tsaka da rubuta jarrabawa. Gudun kar ta rasa jarrabawar ya sanya ta tursasa wa kanta barin asibitin da aka kwantar da ita domin jinya, inda ta dage kan lallai sa ta rubuta jarrabawar.

Ganin yadda take a galabaice da kuma kafiyar da ta yi na za ta rubuta jarrabawar ya sanya aka sanar wa da babban malamin nan, Farfesa Akinkungbe, tsohon shugaban jami’ar Jami’ar Ibadan da Ahmadu Bello, lamarin.

Hakan ya ɓata wa farfesan rai. Nan take ya ce a kira ta, inda ya yi mata faɗa a kan irin wannan gangancin.

Farfesan ya ce mata: “Ke sakariyar yarinya, koma a lura da lafiyarki yadda ya dace. Lafiyarki ta ta fi muhimmanci. Za mu shirya miki jarrabawa daga baya!”

Yarinyar ta ji matukar daɗi tare da yabawa. Cikin ikon Ubangiji daga baya Shugaban Ƙasar Nijeriya na mulkin soji, Janar Yakubu Gowon, ya zamo mijinta.

Wata rana ta kai ziyarar aiki jami’ar. Domin yi mata tarbar girmamawa da nuna maraba, dukkan manyan jami’o’in jami’ar, ciki har da Farfesa Akinkungbe, suka hau layi.

Tana cikin gaishe su ɗaya bayan ɗaya ne ta isa inda farfesan yake tsaye. Cikin girmamawa ta ce, “Yallaɓai, ka tuna ni?”

“E, na tuna ki, Ranki-Ya-Daɗe,” farfesan ya amsa.

“Wannan sakaryar yarinyar nan taka,” uwar gidan shugaban ƙasar ta faɗa cikin annashuwa. Daga nan ta durƙasa a gabansa cikin girmamawa kamar yadda take yi a sa’ilin da tana ɗaliba. “Na gode sosai, Yallaɓai.”

Shi ma farfesan ya ruƙƙufa cikin girmamawa ya ce, “Madalla, Ranki shi daɗe.”

Allah ne kawai ya san gobe…

Ka yi mu’amala da kowa cikin girmamawa.

Fassarawa: Yasir Kallah

Related Posts

Leave a Comment