Home Labarai Babu Wanda yake son yaki, amma dage takunkumi a jamhuriyar Nijar zai ta’allaka ne da yanayin gudun r uwan masu juyin mulki.

Babu Wanda yake son yaki, amma dage takunkumi a jamhuriyar Nijar zai ta’allaka ne da yanayin gudun r uwan masu juyin mulki.

by masta


Shugaban Kasa Bola Tinunu ya ce sai an bi duk wata hanyar diflomasiyya ba a samu nasara ba ne za a duba yiwuwar amfani da karfin soji a kan masu juyin mulkin Jamhuriyar Nijar, inda ya kara nanata cewa ba za su taba aminta da hambare zababbabiyar gwamnati ba.
Shugaba Tinunu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci a Najeriya, karkashin jagorancin Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III a Fadar Shugaban Kasa, inda ya ce lallai ba a yi watsi da yiwuwar amfani da karfin sojin ba.
“Ina godiya gare ku bisa kai-koma da kuka yi ta yi zuwa Jamhuriyar Nijar, amma Mai alfarma akwai bukatar ku sake komawa. Fargabar da nake yi ta yiwuwar fara yunkurin gwada irin abin da ya faru a Nijar idan ba mu dakatar da su ba, ya faru a kasar Gabon. Mu da Nijar makwabta juna ne. Babu wanda yake son yaki. Mun ga yadda yakin yake susuta kasashen Ukraine da Sudan. Amma idan ba mu rufe ido mun yi abin da ya kamata ba, dukkanmu za mu sha wahalar abin da zai biyo ba,” inji shi.
Shugaba Tinunu ya bayyana cewa a zamanin mulkin Janar Abdulsalami Abubakar ne ya aiwatar da tsare-tsaren mayar da mulki hannun farar hula a wata tara a shekarar 1998, wanda wannan ne ya yi sanadiyar mayar da kasar zuwa ga mulkin dimokuradiyyar da muke ciki a yanzu. Wannan ya sa Shugaban Kasa Tinubu yake ganin babu dalilin da zai sa ba za a iya aiwatar da irin haka a Nijar ba, idan har sojojin Nijar din da gaske suke.
‘Mai alfarma, don Allah kar ku gaji. Za ku sake komawa. Abin da sojojin nan suke yi ba zai taba sabuwa ba. Idan sun yi gaggawar kawo hanyoyin maslaha, hakan ne zai ba mu damar saukaka wa kasar Nijar wahalhalun da suke ciki ta hanyar janye takunkumin da muka kakaba mata,” inji shugaban.
A game da radadin da ‘yan Najeriya suke fuskanta bayan cire tallafin man fetur, shugaban ya tabbatar da cewa gyare-gyaren da yake yi za su zama alheri ga kasar ta hanyar habaka tattalin arzikinta, wanda zai amfanar da mafiya yawan ‘yan kasar musamman wajen inganga ababen more rayuwa da kiwon lafiya da ilimi.
“Najeriya ta riga ta hau hanyar tudun mun tsira. Lallai alamu sun nuna cewa akwai haske a gaba. Za mu gina kasar da ‘ya’yanmu da jikokinmu za su yi alfahari da mu.”
Shugaban Kasar ya bayyana wa tawagar cewa Gwamnatin Tarayya ta fara tattaunawa da gwamnonin jihohi domin samar da filayen noma da kiwo na zamani domin samar da wajajen noma da kiwon ababen da za a riga fitarwa zuwa kasashen waje sannan ya samar da ayyukan yi, kuma kasar ta samu kudin shiga.
“Idan har Najeriya za ta cigaba da neman riga-kafin wasu cututtuka; idan ana cigaba da samun mutuwar mata da jarirai wajen haihuwa, lallai ke nan akwai bukatar gyara. Zan cigaba da tattaunawa da jagorori irin ku domin biya wa al’ummarmu bukatunsu,” inji shi.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya ce Shugaban Kasar ya ware Naira biliyan 50 domin cigaba da sake gina yankin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma tare da duba yiwuwar samar da zaman lafiya cikin sulhu da lumana.
A nasa jawabin, Mai alfarma Sarkin Musulmi ya tabbatar wa Shugaban Kasar cewa suna tare da shi 100 bisa 100, inda ya ce lallai shugaba yana samun matsayi ne da yardar Allah ba ta mutum ba.
Mai alfarma Sarkin Musulmi ya tabbatar wa Shugaban Kasar cewa majalisarsu a shirye take ta cigaba da ba shi shawara da goyon baya domin ciyar da kasar gaba. “Allah zai tambayi dukkan shugaba a kan nauyin da aka daura masa.”
Sannan ya bayar da shawarar cewa a sa ido sosai a kan tallafin rage radadin da ake yi a fading kasar sosai, sannan ya bukaci a yi kari ga inda bai kai ba.
“Ina da yakinin cewa za mu fita daga wannan yanayin da muke ciki,” inji Sarkin Musulmi.

Chief Ajuri Ngelale
Mai ba Shugaban Kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai.

August 31, 2023

Related Posts

Leave a Comment