Home Labarai Barayin waya sun shiga hannu a Katsina

Barayin waya sun shiga hannu a Katsina

by masta

WASU ƁARAYIN WAYA SUN SHIGA HANNU

Yadda Aka Cafke Ɓarayin Waya A Katsina.

Rundunar ‘Yansandan jihar Katsina, ta sanar da kama wasu shahararrun ɓarayin waya su biyu, waɗanda suka daɗe suna aikata satar wayoyin jama’a a cikin garin Katsina.

Dubun waɗannan shahararrun ɓarayin waya ya cika ne, a lokacin da suka shiga wani shago tare da sace wayoyin hannu har guda arba’in da takwas 48.

Kakakin rundunar ‘Yansandan jihar Katsina SP Gambo Isa ya ƙara da cewa, babu wani ɗan fashin wayar da za su ɗaga wa ƙafa, za su shiga farautar masu ƙwacen wayoyin jama’a a duk wani lungu da saƙo na ciki da wajen jihar. Don haka ya ce, duk masu aikata wannan mummunar ta’ada su shiga taitayinsu.

Haka nan SP Gambo Isah ya yi kira ga jama’ar jihar Katsina da su kai rahoton duk inda suka ga ana ƙoƙarin yi wa jama’a ƙwacen waya.

Daga: Nafiu Salisu

Related Posts

Leave a Comment