Home Labarai Matsalar Tsaro a Nijeriya Kasar ta ci baya

Matsalar Tsaro a Nijeriya Kasar ta ci baya

by masta

MUNA BUƘATAR KWANKWASO A APC

Bashir Ahmad Ya Bayyana Farin Cikinsa Kan Ganawar Kwankwaso Da Tinubu.

Hadimin shugaban ƙasa kan kafafen sada zumunta Bashir Ahmad, ya ce za su yi maraba da tsohon Gwamnan Jihar Kano, kuma tsohon Sanata Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso zuwa cikin jam’iyyar APC.

Bashir Ahmad ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da manema labarai. Ya ce, Suna maraba da Kwankwaso zuwa APC ne saboda suna buƙatar tsayayyen jagora a Kano.

A baya-bayannan dai an ga yadda maganganu da hotuna gami da video na ganawar zaɓaɓɓen shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu da tsohon Gwamnan Kano, kuma madugun jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso suka karaɗe shafukan sada zumunta.

Ganawar da wata majiya ke nuna rashin jin daɗinta ga wasu ‘yan jam’iyyar APC musamman a jihar Kano, har ma da gwamnati mai barin gado.

Abin jira dai a gani shi ne, shin jagoran NNPP ɗin zai haɗe da jam’iyyar APC ne da gwamnatin Tinubu ko a a?.

Daga: Nafiu Salisu

Related Posts

Leave a Comment