
Takaitaccen Tarihin Sheikh Muhammad al Kashnawi al Fallati (wani masanin lissafi)
An haifi Muhammad bin Muhammad al Kashnawi al Danrankawi a garin Danranko, sai dai ba a san wace shekarar da aka haife shi ba, saboda bacewar littafin tarihinsa da ya rubuta da kansa, maisuna al Rihla. Amma dai ya rasu a Gidan Hasan al Jabarti, a Misra a shekarar 1741.
Yayi karatu a hannun malamai da dama, kamarsu; Muhammad al Wali bin Sulayman al Fallati, da su Sheikh Muhammad Bindu, da Sheikh Muhammad Fodiyo, da kuma sheikh Hashim (Bazamfari).
Koda yake ya karanta fannoni da dama, amma yafi maida himma a bangaren lissafi, hisabi, aufaq (magic Square) da kuma wasu bangarori da suka shafi najm da kimiyyar taurari.
Ya sha yawo domin neman ilmi gari zuwa gari, amma ya fada a wani littafinsa cewa ” duk kokarinsa na neman ilmi, sai da ilmi ya gajiyar da shi. In nayi tunanin na kammala, sai in ga wani abu sabo da ban san shi ba”
A shekarar 1730 ya bar kasar Hausa, ya tafi aikin Haji a Hijaz. Bayan shekara uku ko hudu, ya koma kasar Misra da zama, inda ya bakunci babban abokinsa Hasan Al Jabarti. An tabbatar da baa samu Wanda ya tara littattafai kuma ya karance su kamarsa ba. Ya bayyana cewa, bai taba aron littafi ba, sai yayi kkwafe littafin, kuma yayi masa sharhi. A wannan zaman ne ya kammala rubuta Bakandamiyar littattafansa maisuna Durr al Manzum a Cairo.
Kadan daga littattafansa sun hada da:
Bahajatal al faq wa idah al lubs Wanda ya rubuta akan ilmin huruf, Wanda wasu me kira mugni wal mawafi.
Ya kuma rubuta
Barnamaj shuyukhihi, akan malamansa da yayi karatu a wurinsu
Da
Bughayatul mawali fi tarjamat Muhammad wali: akan tarihin malaminsa Muhammad na Wali
Da
Bulughul Arab, fi Kalam al Arab, akan nahawun larabci
Da
Duraral yawaqit fi ilm al huruf wal asma
Da
Al Durr al manzum wa khulasat al sirr al makhtum fi ilm al talasim wal nujm . Wanda ya rubuta bayan da wani shehin malami a Makka ya roke shi arzikin ya rubuta, maisuna Ismail bin hamza al Duhaydih, shi kuma wani malami ne Bahaushe a Makka a lokacin da ake kira; Yunus bin Muhammad al Hausawiy al Kanawi ya hada su.
Sai kuma
Tahriratal ra’iqa
Akan rayuwar manzon Allah bayan mutuwarsa.
Wadannan kadan ne daga gudunmowar wannan bajimin malami.
Abdurrahman al Jabarti ya bayyana malam al Kashnawi a littafinsa maisuna: al Aja’iba al Ashar fi al Tarajim da
” koluluwa, gwani, kogin ilmi, Bahrin fannoni, Wanda ba ayi kamarsa ba, kuma taska ta kimiyya da ilmomin sirri da haqiqa”
Allah ya karbi ran wannan malami a shekarar 1741, shekara kusan goma sha daya bayan rasuwarsa malaminsa Muhammad al Wali.

